Fifa ta kare Jonas Eriksson

Jonas Ericksson Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasan da Pellegrini ya ce Alkalin wasa ya goyi bayan Barcelona

Shugaban alkalan kwallon kafa na Fifa ya kare zargin da kocin Manchester City ya yi wa Jonas Ericksson cewa ya goyi da bayan Barcelona a wasan kofin zakarun Turai da suka kara ranar Talata.

Erikson ya bai wa Barcelona fenariti sannan ya kori dan wasan City Martin Demichelis a karawar da aka doke su da ci 2-0 a Ettihad.

Kocin dan Chile ya kuma ce ba shi da kwarewa saboda ya fito ne daga Sweden.

Sai dai mataimakin shugaban Fifa Jim Boyce ya ce "maganar banza ce a ce ba za a zabi alkalin wasa ba saboda ya zo daga karamar kasa."

Erikson, mai shekaru 39 na daga cikin wadanda za su alkalanci kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.