Fletcher zai takawa Scotland leda

Darren Fletcher Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Rabon da dan wasan ya bugawa Scotland kwallo tun 2012

Scotland ta gayyaci dan wasan Manchester United ,Darren Fletcher, domin shiga tawagarta da za ta buga wasan sada zumunci da za ta kara da Poland a watan gobe.

Dan wasan, mai shekaru 30, mai wasan tsakiya zai koma tawagar ne bayan doguwar jinya da ya yi.

Fletcher zai buga wa Scotland wasan da za ta yi a birnin Warsaw na Poland ranar biyar da Maris -- kuma rabonsa da bugawa kasar wasanni tun a shekarar 2012.

Dan kwallon Dundee United Andrew Robertson zai bugawa kasar wasan farko bayan da ya samu takardar gayyata.

Shi ma dan wasan Sunderland Phil Bardsley yana cikin tawagar 'yan wasan kasar.

Fletcher mai wasan tsakiya ya bugawa kasar wasanni 61.