'Korar Szczesny ne ya kashe wasa'

Wojciech Szczesny Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dai kori mai tsaron ragar Arsenal ne kafin a tafi hutu

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya yi imanin cewa jan katin da aka baiwa Wojciech Szczesny ne ya kashe wasan su da Bayern Munich.

Arsene Wenger ya kuma zargi dan wasan Bayern Munich Arjen Robben da janyo abinda ya faru.

An dai kori mai tsaron ragar ne kafin a tafi hutu, a wasan da Arsenal din ta sha kashi a hannun Bayern da ci 2-0 a gida ranar Laraba.

Shi dai Alkakin wasan ya zargi mai tsaron gidan Arsenal dinne da neman kafar Arjen Robben abinda ya sa ya sallame shi daga wasan.

Karin bayani