Fulham ba za ta fadi ba - Magath

Felix Magath Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin yace za su fafata don ganin an gudu tare a tsira tare

Sabon kocin Fulham Felix Magath ya ce yana da tabbacin cewa kungiyarsa ba za ta fadi daga gasar Premier ba, har yana harin lashe wasanni shida a gaba.

Kungiyar wacce ta sallami kocinta Rene Meulensteen da mataimakansa, tana matsayi na karshe a teburin Premier, maki hudu take nema domin ci gaba da zama a gasar.

Magath, mai shekaru 60, ya ce "Ina da tabbacin ba zamu fado daga gasar Premier ba, za mu ci gaba da fafutuka tare."

Wasu daga cikin tsofaffin 'yan wasa da suka hada da tsohon dan kwallon Norway jan Aage Fjortoft da suka yi kwallo lokacin da ya horas da Eintracht Frankfurt, ya ce kocin yafi yadda da da'a da kwazon dan kwallo.