Ireland ba ta gayyaci Given wasa ba

Shay Given Hakkin mallakar hoto inpho
Image caption Kocin tawagar ya tattauna da 'yan wasan biyu tawayar tarho

Kocin tawagar Jamhuriyar Ireland Martin O'Neill bai gayyaci Shay Given da Stephen Ireland wasan sada zumunci da za su kara da Serbia a ranar 5 ga Maris ba.

Given, mai shekaru 37, ya yi ritaya daga bugawa Ireland wasa bayan kammala gasar kwallon nahiyar Turai a 2012, sai dai an danganta cewa zai dawo buga mata kwallo.

Golan Aston Villa dake wasan aro a Middlesbrough yarjejeniyarsa za ta kare a karshen mako da kungiyar.

Rabon da Ireland ya bugawa kasarsa wasa tun lokacin da ya yi karyar mutuwar kakanninsa da ya fice da tawagar 'yan wasa a shekarar 2007.

Da yake sanar da sunayen tawagar 'yan wasan ranar Alhamis, O'Neill ya ce ya tattauna da Given da kuma Ireland ta wayar tarho.