An yi wa Dike tiyata a agara

Bright Dike
Image caption Dan wasan ya sanar da cewa anyi masa aiki cikin nasara

An yi wa dan wasan Najeriya mai zura kwallo a raga Bright Dike tiyata a raunin da ya ji a agararsa.

Dike wanda yake tawagar 'yan wasan Najeriya da za ta kara da Mexico ranar 5 ga Maris, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar an yi masa tiyatar cikin nasara.

Sai dai ba a sani ba idan dan wasan mai shekaru 27 zai samu sauki kafin a fara gasar kofin duniya da Brazil zata karbi bakunci daga 12 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.

Kocin Najeriya Stephen Keshi ya ce "za mu yi matukar rashin dan wasan matuka idan har ba zai samu buga kofin duniya ba".