Rangers za ta karbi lamunin kudi

Rangers Stadium Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Kungiyar na kokarin ganin ta cigaba da guganar da harkokinta

Kungiyar Rangers ta bada sanarwar tattaunawa da masu hannun jari domin karbar lamunin £1.5 miliyan domin ci gaba da gudanar da kungiyar.

Kungiyar ta bada tabbacin ne a kasuwar hannun jari cewa ba a kai da cimma yarjejeniya ba.

Tun a farkon watannan babban jami'in kungiyar Graham Wallace ya karyata boye bayanai da rashin tabbas, sai dai ya ce kungiyar na daf da kasa biyan bashin da ake binta.

Kungiyar ta bada rahotan faduwa na gudanar da kungiyar da ya kai £14 miliyon a watanni 13 zuwa Yuni bayan da ta kara shiyar £22 miliyon a shekarar 2012.