Rooney ya sabunta kwantiragi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Da farko dangantaka ta yi tsami tsakanin Rooney da Moyes

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar tasa , inda zai rika karbar kusan dala dubu 500 a sati daya zuwa 2019.

A yanzu zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa akalla watan Yuni na 2019.

Rooney me shekara 28, ya shiga kungiyar ne a 2004, kuma kawo yanzu ya jefa mata kwallaye sama da 200.

A kakar da ta gabata Manchester United ce ta dauki Kofin Premier amma a yanzu ita ce ta bakwai a teburin gasar, karkashin sabon mai horad da 'yan wasanta, Dvid Moyes.

Karin bayani