An raba jaddawalin neman gurbin Euro 2016

Scotland da Jamhuriyar Ireland na ruku daya a wasan neman gurbin kofin Nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a shekarar 2016.

Sauran kasashen da suke rukunin sun hada da Jamus da Poland da Georgia da Gibraltar.

Ingila za ta kara da Switzerland da Slovenia da Estonia da Lithuania da kuma San Marino yayin da Wales na rukuni daya da Bosnia-Hercegovina da Belgium da Israel da Cyprus da kuma Andorra.

Ireland ta Arewa na rukuni na shida da ya kunshi Greece da Hungary da Romania da Finland da tsibirin Faroe.

Faransa mai masaukin baki tuni ta samu damar shiga gasar da zai rage sauran kasashe 23 da za su cike gurbi, bayan da aka samu karin akan kasashe 16 da suke shiga gasar a baya.

Daga cikin rukunnai tara da aka raba, na daya dana biyu a kowanne rukuni za su sami gurbin shiga gasar, sannan a dauko kasashe takwas daga rukunnan da suka yi kokari domin buga wasan cancanta a tsakaninsu a watan Nuwambar 2015.

Mai rike da kofin Spain tana rukuni da ya kunshi Ukraine da Slovakia da Belarus da Macedonia da Luxembourg.

Ga yadda aka raba rukunnan

Group A: Netherlands, Czech Republic, Turkey, Latvia, Iceland, Kazakhstan.

Group B: Bosnia-Hercegovina, Belgium, Israel, Wales, Cyprus, Andorra.

Group C: Spain, Ukraine, Slovakia, Belarus, FYR Macedonia, Luxembourg.

Group D: Germany, Republic of Ireland, Poland, Scotland, Georgia, Gibraltar.

Group E: England, Switzerland, Slovenia, Estonia, Lithuania, San Marino.

Group F: Greece, Hungary, Romania, Finland, Northern Ireland, Faroe Islands.

Group G: Russia, Sweden, Austria, Montenegro, Moldova, Liechtenstein.

Group H: Italy, Croatia, Norway, Bulgaria, Azerbaijan, Malta.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jaddawalin neman shiga gasar kofin Nahiyar Turai

Group I: Portugal, Denmark, Serbia, Armenia, Albania.