Fulham ba za ta fadi a Premier - Magath

Felix Magath
Image caption Kocin ya bugi kirji cewa za su ci gaba da buga gasar Premier

Sabon kocin Fulham Felix Magath ya kara jaddada cewa zai jagoranci kungiyar ta ci gaba da buga gasar Premier duk da kasa doke West Brom a wasansa na farko da suka ta shi 1-1.

Ta shi wasa 1-1 da suka yi ranar Asabar na nufin kungiyar za ta ci gaba da zama a matsayi na karshe a teburi, tana neman maki hudu domin ci gaba da buga gasar Premier kuma saura wasanni 11 a kammala gasar bana.

Da aka tambayi kocin ko kungiyar za ta fado daga gasar Premier bana, sai ya ce "Na tabbata ba za mu fadi ba, zanyi iya kokori naga munci gaba da buga gasar."

Magarth ya kara da cewa "Daf ya rage mu doke West Brom amma wasan gaba za muyi nasara - kuma Chelsea za mu doke."

Sabuwar fasahar da ake sawa a cikin raga ce ta tabbatar da farke kwallon da West Brom tayi lokacin da kwallo ta haura layin raga golan Fulham Maarten Stekelenburg ya fito da ita.

Magath bai taba jagorantar kungiya ta fadi daga league ba tsawon shekaru 20 da ya horas a Jamus, ya kuma maye gurbin Rene Meulesteen a Craven Cottage ranar 14 ga Fabrairu da nufin ceto kungiyar kada ta fadi daga gasar Premier a bana.