Liverpool ta doke Swansea da ci 4-3.

Sturridge Sterling
Image caption Bayan wasannin mako na 27 Liverpool na matsayi na hudu a teburin Premier

Kungiyar Liverpool ta doke Swansea a Anfield da ci 4-3 a wasan mako na 27 a gasar kofin Premier.

Jordan Henderson ne ya zura kwallaye biyu daga cikin wadanda ta zura wa Swansea da yasa har yanzu Liverpool take matsayi na hudu a teburin Premier.

Daniel Sturridge ne ya fara zura kwallo a ragar Swansea a minti na biyu da fara wasa, daga baya Henderson ya zura kwallo ta biyu a raga.

Swansea ta fara farke kwallo farko ta hannun Jonjo Shelvey da ya buga kwallo tun daga yadi na 20 ta fada raga, sai Bony da ya zura ta biyu bayan kwallo ta daki kan dan bayan Liverpool Martin Skrtel wasa ya koma 2-2.

Nan take Sturridge ya kara kwallo ta uku a bugun da ya samu ta wajen Suarez, kafin Bony ya sake farke kwallo a dukan Penarity, sannan Henderson ya kara kwallo ta hudu ta kuma karshe da wasa ya tashi 4-3.