Ibrahimovic ya zura kwallaye 3 Rigis

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon ya koma PSG da kafar dama

Zlatan Ibrahimovic ne ya zura kwallaye uku a ragar Toulouse a karawar da suka doke su da ci 4-2 har gida a gasar Faransa wasan mako na 26.

Dan wasan Sweden ya fara zura kwallo a bugun fenarity daga baya Wissam Ben Yedder ya farke kwallo.

Ezequiel Lavezzi ya kara kwallo ta biyu kafin Ibrahimovic ya zura kwallonsa ta biyu da Yohan Cabeye ya bugo masa.

Toulouse ta rage yawan kwallo ta hannun Ben Yedder, nan da nan Ibrahimovic ya zura kwallonsa ta uku.

Dan wasan mai shekaru 32 ya zura kwallaye 37 daga cikin wasanni 36 da ya bugawa PSG a bana.

Nasarar da PSG ta samu yasa ta bada tazarar maki biyar a teburi bayan da Reims ta doke abokiyar hamayyarta Manaco da ci 3-2 ranar Juma a.

Ibrahimovic, ya zura kwallaye shida a wasanni uku baya da ya buga, shi ne jagaba wajen yawan zura kwallo a gasar Faransa, bayanda ya zura kwallaye 22 ya bada tazarar rarar kwallaye tara tsakaninsa da mai biye da shi.