Rodgers ya yaba kokarin Liverpool

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool tana harin neman gurbin gasar kofin zakarun Turai

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya yaba da kokarin 'yan kwallon kungiyar da suke nuna yunwar neman gurbin gasar kofin zakarun Turai a wasannin Premier.

Liverpool ta saka kaimi a karawar data doke Swansea da ci 4-3 a Anfield ranar Lahadi.

Rodgers ya ce "Mun tabbata muna iya zura kwallaye a raga, idan wasa bai mana kyau ba muna sa kaimi da kwazo a kowacce karawa da muke yi."

"Muna kai hare-hare masu zafi da ke taimaka mana lashe wasanni, sai dai ina takaicin kwallayen da ake zura mana."

Liverpool ta samu maki 17 daga cikin 21 da ya kamata ta lashe tun lokacin da Chelsea ta doke ta da ci 2-1 ranar 29 ga Disamba, kuma saura maki hudu tsakaninta da Chelsea mai matsayi na daya a teburi, za kuma ta ziyarci Anfield.

Rodgers na taka tsantsan kan bayyana cewa kungiyarsa za ta iya lashe kofin Premier a bana.