Rangers ta karbi lamuni daga Easdale da Laxey

Sandy Easdale Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Shugaban na ta fadi tashi na ganin kungiyar bata ruguje ba

Kungiyar kwallon kafa ta Rangers ta bada sanarwar karbar lamunin £1.5 miliyan daga shugabanta mai hannun jari Sandy Easdale da kuma kamfanin Laxey Partners Ltd.

Shugaban zai bada £500,000, sai kamfanin zuba jari ya samar da sauran kudin.

Kungiyar ta bada sanarwar yin asarar £14.4 miliyon a watanni 13 baya zuwa watan Yuni, kuma 'yan wasa sunki amincewa da a zabtare musu albashi na kashi 15 daga cikin dari.

Rangers ta ce za tayi amfani da kudin wajen manyan ayyukan kungiyar, daga nan zuwa wata mai kamawa.