Sochi 2014: Russia ta lashe azurfa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An shafe mintina 130 ana gudanar da kasaitaccen bikin rufe wasannin

Kasar data karbi bakuncin wasannin Olympic Russia ita ce sama a teburin Kasashen da suka sami kyautar lambar azurfa yayinda aka kamaala wasannin a ranar Lahadi,

An dai shafe kwanaki 17 ana wannan gasar.

Shugaban kwamitin gasar Olympic na duniya Thomas Bach ne ya rufe wasannin a hukumance a lokacin wani kasaitaccen biki na mintina 130 da aka gudanar

An baiwa Koriya ta Kudu tutar gasar Olympics yayinda Pyeongchang ke karbar bakuncin wasannin a shekarar 2018