Kiris ya rage a ba mu kofi - Muller

Thomas Muller Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya bugi kirji da cewa suna kan ganiyarsu

Dan kwallon Bayern Munich mai wasan gaba Thomas Muller ya ce ba abin da zai hana su kara lashe kofin da suka dauka a bara na Bundesliga.

Mai rike da kofin zakarun Turai ta bai wa Bayern Leverkusen, mai matsayi na biyu, tazarar maki 19 da ya rage wasanni 12 a kammala gasar bana, ta kuma lashe wasanni 47 a jere a Bundesliga.

Muller ya ce "duk wanda yake bibiyar Bundesliga ya san mu ne za mu lashe kofin bana -- ganin yadda muke lashe wasanni, lokaci ake jira a ba mu kofinmu."

Dan kwallon Jamus, mai shekaru 24, ya zura kwallaye biyu a karawar da Munich ta doke Hannover da ci 4-0 ranar Lahadi, koda yake ya ji rauni a wasan da zai yi jinyar kwanaki biyar.