FA za ta fara sauraren kara kan Anelka

Nicolas Anelka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nunin da FA take tuhumar Anelka da ya ce ya kwaikwayi abokinsa ne

Hukumar kwallon kafar Ingila za ta fara sauraren kara a kan Nicolas Anelka daga ranar Talata bisa nuni da ya yi da hannunsa da aka alakanta da goyon bayan 'yan Nazi.

Dan kwallon West Brom mai zura kwallo a raga mai shekaru 34, ya karyata tuhumarsa da ake cewa ya yi nunin ne da nufin cin mutunci da rashin da'a da kuma rashin sanin ya kamata a karawar da suka tashi canjaras da West Ham a watan Disamba.

Tsohon dan kwallon Faransa zai fuskanci hukuncin dakatarwa daga buga wasanni biyar idan an same shi da laifi.

An kafa kwamitin mutane uku da za su duba shaidu daga bangaren lauyoyin FA da na Anelka.

Dan kwallon ya nace cewa shi dai ya yi nunin ne don goyon bayan abokinsa dan Faransa mai barkwanci, Dieudonne M'bala M'bala, wanda shari'a ta zarga da goyon bayan 'yan Nazi.

Ana sa ran kammala sauraren ba'asi ranar Juma'a