Boye da Mensah sun dawo kwallo

Boye  Mensah
Image caption Ghana na kokarin ganin ta taka rawar gani a kofin duniya

'Yan wasan Ghana masu tsaron baya, John Boye da Jonathan Mensah, sun koma tawagar 'yan wasan kasar domin buga wasan sada zumunci da Montenegro ranar Laraba, 5 ga Maris bayan da suka yi jinya.

Kocin tawagar Ghana, Kwesi Appiah, bai dauki mai tsaron gida Fatau Dauda ba sakamakon kasa bugawa kungiyarsa ta Orlando Pirates da ke Afirka ta kudu wasanni akai-akai.

Haka kuma bai gayyaci tsohon dan kwallon AC Milan mai zura kwallo a raga ba Dominic Adiyiah.

Bayan karawa da Montenegro a Podgroica, Ghana za ta fafata da Netherlands ranar 31 ga Mayu.

A gasar kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci Ghana na rukuni na bakwai da ya kunshi Jamus da Portugal da Amurka.

Ga 'yan wasan da Ghana ta gayyato

Masu tsaron raga: Stephen Adams (Aduana Stars), Adam Kwarasey (Stromgodset)

Masu tsaron baya: David Addy (Vitoria Guimaraes), Harrison Afful (Esperance), Jerry Akaminko (Eskisehirspor), John Boye (Stade Rennes), Samuel Inkoom (Platanias), Jonathan Mensah (Evian Thonon Gaillard FC), Daniel Opare (Standard Liege)

Masu wasan tsakiya: Albert Adomah (Middlesbrough), Emmanuel Agyemang Badu (Udinese), Kwadwo Asamoah (Juventus), Christian Atsu (Vitesse Arnhem), Andre Ayew (Olympique Marseille), Michael Essien, Sulley Muntari (both AC Milan), Mubarak Wakaso (Rubin Kazan)

Masu zura kwallo: Jordan Ayew (Sochaux), Kevin Prince Boateng (Schalke 04), Asamoah Gyan (Al Ain), Abdul Majeed Waris (Valenciennes).