Newcastle ta ci ribar fam £9.9 miliyan

Newcastle United Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da kungiyar ta sayo Manyan 'yan wasa tun 2013

Newcastle ta ce cinikayyar 'yan kwallo da ta yi na daga cikin dalilan da ta samu karin ribar kashi 600 bisa dari, bayan an cire haraji ya zuwa watan Yunin 2013.

Kungiyar ta ce ta samu karin ribar £9.9miliyan bayan an cire haraji, kari a kan £1.4 miliyan da ta samu a shekarun 2011/12.

Ta kara da cewa ta samu £28.7 miliyan a cinikayyar manyan 'yan kwallo data sayar a 2012-13 da suka hada da Leon Best da Fraser Forster da Demba Ba.

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar sun zarge ta kan gaza sayo manyan 'yan wasa, tun Yunin 2013

Masu zura kwallo a raga Luuk de Jong and Loic Remy su ne 'yan wasan da kungiyar ta dauka aro daga Borussia Monchengladbach da QPR, sannan ta sayar da Yohan Cabaye ga Paris St-Germain kan kudi £19m a Janairu.