Moyes ya dau alhakin wasan su

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Olympiakos ta lallasa Manchester United da ci 2-0

Manajan kulab din Machester United David Moyes ya dau alhakin kashin da suka sha a hannun Olympiakos.

Olympiakos dai ta ci Manchester United da ci 2-0

Manchester United dai sune na shida a League.

Moyes ya ce “ na dau alhakin abinda ya faru. Lokaci na ne, a kodayaushe zan tunkari hakan”.

Ya kuma kara da cewa basu taka rawar gani ba, kuma ya ce wannan shine wasa mafi muni da suka buga a Turai.