Ribar Newcastle ta karu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Newcastle su soki gazawar Kulab din wajen daukar ‘yan wasa na dindindin

Kulab din Newcastle ya danganta ‘cinikin dan wasa’ a matsayin daya daga cikin dalilan da ya samu karin riba bayan kammala biyan haraji .

Kulad din ya ce ya samu ribar sama da £9m bayan biyan haraji a shekarar 2013.

Kulab din Newscatle ya ce kudaden da ya kashe har £28.7m akan manyan ‘yan wasa shida a shekarar 2012-13 sun fito ne daga sayar da ‘yan wasa kamar su Leon Best da Fraser Forster da kuma Demba Ba.

Wasu magoya bayan kulab din dai sun soki gazawar Newscatle wajen daukar ‘yan wasa na dindindin tun daga watan Yunin shekarar 2013