An tsaida ranar fara League a Najeriya

Nduka Irabor
Image caption Irabor da ya dage sai ya gyara yadda ake gudanar da kwallo a Najeriya

Kamfanin dake kula da gudanar da gasar Premier a Najeriya (LMC) ya bada sanarwar fara gasar bana da za a fara ranar 7 ga Maris a kakar wasan 2013/14.

Gasar ya kamata a ce an fara ta makon da ya wuce, rikita - rikita tsakanin Kamfanin da kungiyoyin yasa aka dinga dage gasar a watanni baya.

Rashin jituwar dake tsakanin bangarorin biyu ya faro ne akan yiwa 'yan wasa lasisi da zai kara mayar da kungiyoyin cikin rukunnan kwararru.

An fid da sabuwar ranar fara gasar bana ne a taron da aka gudanar tsakanin LMC da wakilin kungiyoyin kwallon kafar su 20.

Sun cimma yarjejeniya cewa kungiyoyin za su biya kudin yin rijista Naira Miliyan 100 domin buga gasar kakar bana.

Kungiyoyin za su iya fara biyan kudin kaso daya bisa hudu kimanin Naira miliyan 25, biya hudu.

An baiwa kungiyoyin damar kammala rijistar 'yan wasa daga nan zuwa 4 ga Maris, idan har ba su kammala ba za a rage musu maki shida da kwallaye shida sannan a rike kudin kasonsu na kudin tallar da aka samu na gasar.