Ancelotti ya yabi Gareth

Image caption Bale ya zura bala- balai 14 a wasanni 23

Manajan kulab din Real Madrid Carlo Ancelotti ya yabi Gareth Bale bayan wasan da suka taka da Schalke inda ya ce dan wasan ya taka wasan da yafi kowanne kyau a kakar wasannin.

Real Madrid dai ta lallasa Schalke da ci 6-1.

Bale ya zura kwallaye biyu a raga a wannan wasan.

"Wannan shine wasan Bale mafi kyau" in ji Anceloti

Bale dai ya zura bala balai 14 a raga a wasanni 23 da ya taka tun daga lokacin da ya sannin kwanturagin £85.3m daga kulab din Tottenham a watan Satumba