Jagielka ba zai bugawa Ingila wasa ba

Phil Jagielka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya gamu da tsagewar tsoka a cinyarsa

Dan kwallon Everton mai tsaron baya Phil Jagielka, ba zai bugawa Ingila wasan sada zumunci da za ta kara da Denmark ranar 5 ga Maris ba, sakamakon rauni da ya ji.

Kocin Everton Roberto Martinez, ya ce dan kwallon mai shekaru 31, ya gamu da tsagewar tsoka ne, kuma ba zai buga karawar da kungiyar za tayi da West Ham ba.

Kocin Ingila Roy Hodgson, zai sanar da tawagar 'yan wasa 30 ranar Alhamis da za su buga wasan.

Martinez ya kuma bada shawarar cewa ya kamata kocin Ingila ya gayyaci Gareth Barry cikin tawagar 'yan wasan.