Za a yi wa Lacina Traore tiyata

Lacina Traore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Damar da dan wasan ya samu a Everton na masa ta leko ta koma

Zaman dan kwallon Ivory Coast Lacina Traore a Everton da ya je aro daga Monaco zai kawo karshe idan har kungiyar ta amince cewar dan kwallo na bukatar tiyata a kafarsa.

Dan wasan mai shekaru 23, ya ji raunin ne kafin karawar da kungiyar ta yi da Chelsea a ranar Asabar.

Roberto Martinez ya ce "Raunin dan wasan yana bukatar tiyata -- Mataki ne mai tsauri da za mu fuskanta.

"Idan har sai an yi masa aiki a kafarsa da zai yi jinyar wata biyu zuwa uku, to lallai ya gama buga mana wasanni kenan."

Traore ya koma Everton ne a Janairu lokacin yana jinyar tsagewar tsoka, sai dai ya samu sauki harma ya buga wasan farko ya zura kwallo a karawar da suka doke Swansea a kofin FA da ci 3-1.