Brazil: 'Yan Ingila zasu je da mata

Hakkin mallakar hoto Getty Images Sport
Image caption 'Yan wasan Ingila za su iya tafiya Brazil da matansu

Kocin 'yan wasan Ingila Roy Hodgson ya sanar cewa ba zai hana 'yan wasansa tafiya da matayensu ba zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Wanda ya gada Fabio Capello ya haramtawa matan 'yan wasan halartar gasar cin kofin duniyar a shekara ta 2010.

Hodgson ya ce ya rage ga 'yan wasan su zabi idan har suna son tafiya da matansu.

Ya ce game da Brazil bamu yi dokoki masu tsauri ba.