"Mu ne za mu lashe kofin La liga"

Gerardo Martino Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin ya ce ragamar lashe kofin bana yana hannun Barcelona

Kocin Barcelona Gerardo Martino ya ce su ne za su lashe kofin La liga na Spain a bana, lokacin da suka ziyarci Almeria a karawar da za su yi ranar Lahadi.

Doke Barca 3-1 da Real Sociedad ta yi ranar Asabar ya sa Real Madrid ta ba ta tazarar maki uku, sannan za su ziyarci Bernabeu ranar 23 ga watan Maris.

Martino ya ce "Damar lashe kofin bana tana hannunmu, amma muna bukatar lashe dukkannin sauran wasanninmu da suka rage."

Barcelona ta ajiye manyan 'yan kwallonta a karshen makon da ya gabata, sakamakon nasarar doke Manchester City da suka yi a gasar cin kofin Zakarun Turai, amma kwallIya bata biya kudin sabulu ba a karawar da suka yi da Sociedad.