Man City ta dau kofin Capital One

Man City Capital One Champ Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dama City ta ce kofuna hudu za ta dauka a bana

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya lashe kofinsa na farko a Ingila, bayan da ya doke Sunderland da ci 3-1, a wasan karshe na cin kofin Capital One a karawar da suka yi a filin wasa na Wembley.

Fabio Borini na Sunderland ne ya fara zura kwallo a ragar City a minti na 10 da fara wasa.

City ta yunkuro bayan da aka dawo daga hutun rabi lokaci, ta kuma farke kwallo daga bugun yadi 30 wanda Yaya Toure ya buga tamaula ta fada raga.

Sakwanni 105 bayan da City ta farke kwallon, Samir Nasri ya zura kwallo ta biyu a raga.

Dan wasan Spain Navas wanda ya canji Sergio Aguero a minti na 58 da fara wasa, ya karbi kwallo ta wajen Toure sannan ya buga kwallo ta shiga raga daf da turke.