Newcastle ta ci tarar Pardew £100,000

Alan Pardew Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya yi dana sanin rigima da dan wasan Hull da ya yi

Kungiyar Newcastle United ta ci tarar kocinta Alan Pardew £100,000, ta kuma gargadesa da ya kaucewa sake faruwar dukan dan wasan Hull City David Meyler da ya yi da ka.

Padew, mai shekaru 52, sai da alkalin wasa ya kora shi cikin 'yan kallo a lokacin da abun ya faru, bayan an dawo hutu a karawar da suka dode Hull city da ci 4-1 a KC Stadium.

Kungiyar Newcastle ta fitar da sanarwa cewa " Ta zauna taro da Alan, ya kuma bada hakurin abinda ya faru, kuma ya nuna dana sanin faruwar abin da ya yi.

Hukumar kwallon kafar Ingila FA tace za ta binciki abinda ya faru.