Za a hukunta sakon taguwa a wasan kwallo

Mario Ballotelle Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakon da dan wasan ya nuna lokacin da ya zura kwallo

An cimma yarjejeniyar ce wa za a hukunta duk dan wasan da ya nuna wani sako a taguwarsa lokacin da ake wasan kwallon kafa.

Sashin dake kula da dokakin wasan kwallon kafa na duniya wato (IFAB) ne ya zartar da dokar a taron da aka gudanar a Zurich.

Za a fara gudanar da hukunci daga 1 ga watan Yuni, a lokacin gudanar da gasar cin kofin duniya a Brazil.

Dokar za ta yi aiki ne a yayin gudanar da gasar wasannin kasashe da karawa tsakanin kasashe da kofin duniya.