"Ba za mu sayar da Luis Suarez ba"

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool ta ce bata ga dalilan da zai sa ta sayar da dan wasan ba

Mamallakin kungiyar Liverpool, John Henry, ya tabbatar da cewa a cikin kwantiragin da kungiyar da kuma Luis Suarez suka sanyawa hannu, akwai batun cewa idan wata kungiya za ta iya biyan fam miliyan 40, to za a sayar mata da dan wasan.

Haka shi ma dan wasa Suarez idan zai iya biyan wannan kudin to za a kyale shi ya tafi.

Sai dai kuma kungiyar Arsenal ta taya dan wasan mai shekaru 27, a kan fam miliyan 40 da fam daya a farkon kakar bana, amma ba a sayar musu da shi ba.

Henry ya ce "Tunda mu ne ke da wuka da nama a kan cinikin dan wasan, nan take muka hau kujerar naki."

Tun daga lokacin, Suarez ya sake tsawaita kwangilarsa ta ci gaba da wasa a Anfield har tsawon shekaru hudu da rabi, kuma shi ne yake kan gaba wajen yawan zura kwallaye a Gasar Premier, domin ya zura kwallaye 24--al'amarin da ya kai Liverpool matsayi na biyu a teburin Gasar ta Premier.