Pellegrini na fatan daukar kofuna 3

Manuell Pellegrini
Image caption Kofin Farko da Pellegrini ya lashe tun zuwansa City

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini na fatan daukar kofuna uku, bayan da ya lashe kofin Capital One ranar Lahadi a karawar da ya doke Sunderland.

City ta lashe kofin ne dai da ci 3-1 a karawar da suka yi a filin wasa na Wembley, kuma kofin farko da Pellegrini ya dauka tun komowarsa Ingila horas da kwallo.

Kungiyar za ta kara da Wigan a wasan daf dana kusa da karshe a gasar cin kofin FA, kuma suna cikin kungiyoyin da ke kan gaba a kokarin lashe kofin Premier na bana.

Pellegrini wanda ya maye gurbin Roberto Mancini a matsayin kocin City ya ce "Lashe kofin farko da muka yi, yana da matukar amfani, ta bangare na da mataimakana da kuma 'yan wasa."