Najeriya za ta kara da Scotland

Wani dan wasan Najeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun shekarar 2002 ne dai Najeriya ta yi karawar karshe da Scotland

Najeriya za ta yi wasan sada zumunci da Scotland a London, a yayin da kasar ke shirye-shiryen zuwa gasar cin kofin kwallo na duniya a Brazil.

Za a yi wasan a ranar 28 ga watan Mayu mai zuwa, a filin wasan kulob din Fulham, wato Craven Cottage.

Akwai 'yan wasan Najeriya dake kwallo da dama a nahiyar Turai, don haka ana kallon Scotland a matsayin wata dama ga 'yan wasan dake son shiga tawagar da Steven Keshi zai dauka zuwa Brazil.

Za a yi karawar ce kwanaki shida, kafin Najeriyar ta kara da Girka, a wasan share fagen shiga gasar cin kwallon kafa na duniya na bana.