Mertesacker da Rosicky sun tsawaita kwantiragi

Rosicky Merteserker Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan biyu sun yi murnar tsawaita kwantaraginsu da Arsenal

'Yan wasan Arsenal Per Mertesacker, mai tsaron baya da Tomas Rosicky, sun rattaba hannu na tsawaita kwantaraginsu da kungiyar.

Mertesacker, mai shekaru 29, ya koma Gunners daga Werder Bremen a watan Agustan 2011, ya buga wasanni 42 a kakar wasan bana.

Rosicky, mai shekaru 33, ya koma Arsenal daga Borussia Dortmund a shekarar 2006, kuma kwantaraginsa da kungiyar za ta kare a bana.

Arsene Wenger ya sanar ta shafin intanet din kungiyar ce wa "Yan wasa ne kwararru wadan da suka iya taka leda."