Puyol zai bar Barcelona a bana

Carles Puyol Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya bugawa Barcelona wasanni kusan 400

Kyaftin din Barcelona mai tsaron baya Carles Puyol, zai bar kungiyar a karshen kakar wasan bana.

Mai shekaru 35, kwantaraginsa da kungiyar zai zo karshe ne a shekarar 2016, amma sun cimma yarjejeniya zai iya barin Barca a bana.

Puyol ya bugawa kungiyar wasanni kusan 400, ya fara bugawa Barcelona wasa a shekarar 1999.

Ya lashe kofunan La liga shida da kofin zakarun Turai Uku da kofunan Spaniya biyu tare da kungiyar.

Dan wasan ya kuma taimakawa kungiyar daukar kofin Uefa Super Cup karo biyu da Spaniya Super Cup da suka lashe sau shida.

Haka kuma yana cikin tawagar Spaniya da suka lashe kofin Nahiyar Turai a shekarar 2008 da kuma kofin duniya a shekarar 2010.