Hukumar Premier na tuhumar Cardiff City

Vincent Tan
Image caption Shugaban yana kokarin ganin Cardiff City ba ta fice daga Premier bana ba

Hukumar gudanar da gasar Premier na bin bahasin dalilan da ya sa shugaban Cardiff City Vincent Tan, ya yi tayin baiwa 'yan wasa ladan buga kwallo, domin su kaucewa faduwa daga gasar Premier.

Dan Malaysia ya janye ladan da ya yi niyyar baiwa 'yan wasa kimanin sama da £3.7 Miliyan, lokacin da aka tabbatar masa da ce wa ya saba ka'ida.

Ya kuma yi alkawarin ne kafin su kara da Tottenham, a wasan da aka doke su da ci daya mai ban haushi, a White Hart Lane ranar Lahadi.

Doke su da a kayi ya jefa kungiyar matsayi na 19 a teburin Premier, maki uku tsakaninta da West Brom wacce ke matsayi na 17 mai kwantan wasa daya.

Hukumar Premier ta kayyade duk wasu biyan ladan wasa ya zama yana cikin kwantiragin da kungiya za ta shiga da dan wasa.