Ingila za ta dauki likitan kwakwalwa

Roy Hodson
Image caption Kocin na kokarin ganin Ingila ta lashe kofin duniya a bana

Kocin Ingila Roy Hodson na shirin daukar likitan kwakwalwa Dr Steve Peters, domin taimakawa tawagar lashe kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.

Hodson, zai gayyaci Dr Steve ne, wanda yake tare da Liverpool domin bada shawarwarin yadda 'yan wasan za su tsaida hankalinsu su lashe kofin duniya.

"Yana da kyakkyawan sakamako a fannin wasanni da ya bada gudunmawa, na yi murna zan samu wanda zai da ce da tawagarmu" in ji Hodson.

Peters yana daga cikin wanda ya taimakawa tawagar Ingila samun nasarori a wasan tseren keke a gasar Olympics ta Beijin 2008 da Landan 2012.