Liverpool ta yi asarar £50 miliyan

Liverpool FC
Image caption kungiyar ta bada sanarwar fadu a kakar wasan 2012-13

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, ta sanar da faduwar £50 miliyan a shekarar 2012 zuwa 13, ta kuma ce tana kan hanyar kasuwancin da za ta farfado.

Bashin da ake bin kungiyar a bara ya ragu daga kashi 29 cikin dari zuwa £45.1 miliyan, da samun karin kudin shiga kaso tara cikin dari, kimanin £206.1 miliyan.

Karin kudi £46.8 miliyan da mai kungiyar Fenway Sports Group ya zuba a kulob din, ya taimaka wajen biya bashin filin wasa.

Liverpool na biye da Chelsea a matsayi na biyu a teburin Premier, wacce ke fatan samun gurbin shiga gasar kofin zakarun Turai a kakar wasannin badi.

Rabon kungiyar ta shiga gasar tun a shekarar 2009 zuwa 10, kuma samun gurbin zai taimaka mata samun kudin shiga mai tsoka.