Kamaru za ta kara da Paraguay

Cameroon Friendly
Image caption Kamaru na fatan ganin ta taka rawar gani a gasar kofin duniya

Kamaru ta shirya karawa da Macedonia da Paraguay a wasannin sada zumunci, a shirye - shiryen da take na tunkarar gasar kofin duniya a Brazil.

Wasannin biyu za su buga ne a filin wasa na Kufstein dake Australiya, wurin da Kamaru ta zaba domin karbar atisaye kafin su karasa Brazil.

Kamaru za ta fara karawa da Macedonia ranar 26, ta fafata da Paraguay ranar 29 ga watan Mayu.

An kiyasta cewa hukumar kwallon kafar Kamaru, za ta kashe $540,000 a lokacin da tawagar 'yan wasan za su zauna a Astralia tsakanin 20 zuwa 31 ga watan Mayu.

Kamaru na rukunin farko a gasar kofin duniya da ya kunshi Brazil da Croatia da Mexico, haka kuma Kamaru za ta buga wasannin sada zumunci da Portugal da Jamus da Argentina.