Vidic zai koma Inter Milan a badi

Nemanja Vidic
Image caption Tun a makon jiya dan wasan ya bukaci a bashi izinin barin kungiyar

Kyaftin din Manchester United Nemanja Vidic, zai koma kungiyar Inter Milan ta Italiya, bayan kammala gasar wasan bana.

Tuni Inter Milan ta sanar ce wa dan wasan mai shekaru 32, mai tsaron baya ya rattaba kwantaragi da kungiyar, sai dai ba a bayyana shekaru nawa zai bugawa kulob din wasanni ba.

Vidic, dan Serbia ya sanar da shirinsa na kawo karshen bugawa United wasa ne a watan jiya, bayan da ya kwashe shekaru takwas da rabi a kungiyar.

Ya koma United ne dai a shekarar 2006, ya buga wasanni sama da 200, ya kuma taimakawa kungiyar lashe kofunan Premier biyar.