Porto ta kori kocinta Fonseca

Paulo Fonseca Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Watanni tara kacal kocin ya horas da kungiyar Porto

Mai rike da kofin Portugal Porto, ta sallami kocinta Paulo Fonseca, bayan watanni tara da ya jagoranci kungiyar.

Fonseca, mai shekaru 41, ya rasa aikinsa bayan rashin nasara a wasanni hudu da ya kara, hakan ya maida kungiyar matsayi na uku a teburi da tazarar maki tara tsakaninta da Benfica wacce take matsayi na daya a teburi.

An karya tarihin kasa lashe kungiyar a wasanninta na gida data kafsa tsawon shekaru hudu da rabi, lokacin da Estoril ta doke ta sannan suka tashi wasa 2-2 da Guimaraes ranar Lahadi.

Tuni aka bai wa kocin 'yan wasan kar ta kwana Luis Castro, kungiyar a matsayin rikon kwarya.

Porto ta lashe kofin gasar Portugal karo 27, kuma ita ce zakara a shekaru uku baya.