An dakatar da Adam daga wasanni 3

Charlie Adam Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An dakatar da dan wasan bayan da aka duba fefan bidiyo

An dakatar da dan wasan Stoke City Charlie Adam, daga buga wasanni uku, bayan da FA ta tabbatar da samun dan kwallon da laifin yin keta.

Dan wasan, mai shekaru 28, ya taka kafar dan kwallon Arsenal Olivier Giroud a karawar da suka lashe wasan da ci daya mai ban haushi.

Adam ya karyata zargin, sai dai an same shi da laifin ne bayan da kwamitin mutane uku ya zauna don jin bahasi kan lamarin.

Dan wasan, mai buga tsakiya, ba zai buga karawar da Stoke za ta yi da Norwich da West Ham da Aston Villa ba.