Bale zai buga wasan sada zumunci

Gareth Bale
Image caption Dan wasan ya samu saukin rauni ya kuma dawo ganiyarsa

Kocin tawagar Wales Chris Coleman ya ce Gareth Bale, zai buga karawar da za suyi da Iceland ranar Laraba, kuma da shi za a kammala wasan.

Bale, wanda ya zura kwallaye biyar a wasanni bakwai da ya bugawa Real Madrid ya dawo kan ganiyarsa.

Dan wasan Joe Ledley, ya ji rauni ba zai buga karawar ba, a lokacin da Ashley Williams ya samu sauki aka gayyato cikin tawagar 'yan wasa.

A watan satumba lokacin da Bale ya koma Real Madrid, ya sanar da cewa zai bari dan wasan ya sarara a lokacin da suke buga wasan neman gurbin shiga kofin duniya.