Wilshare zai yi jinyar makwonni 6

jack Wilshere Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan zai yi jinyar makwonni shida kacal

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshare zai yi jinyar rauni na tsawon makwonni shida bayan ya samu karaya a kafarsa ta hagu.

Dan wasan, mai shekaru 22, ya ji raunin ne a lokacin da suka yi karo da dan kwallon Liverpool Daniel Agger, a minti 12 da fara wasan sada zumunci da Denmark.

Koda yake ya ci gaba da wasa har minti 59, kafin a sauya shi a karawar da suka doke Denmark da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Wembley.

Wilshere ba zai buga kofin FA da Arsenal za ta kara da Everton ba a wasan daf dana kusa da karshe da wasan zagaye na biyu a kofin zakarun Turai da Bayern Munich.