Zaben 'yan wasa ya yi wuya - Hodgson

Roy Hodgson
Image caption Kocin na tunanin 'yan wasan da zai zaba zuwa kofin duniya

Kocin tawagar Ingila Roy Hodgson ya ce yana fama da kakanikayin 'yan wasan da zai zaba zuwa gasar kofin duniya a Brazil, bayan da tawagar ta taka rawa a karawar data lashe Denmark.

Daniel Sturrdge ne ya zura kwallo daf da a tashi wasa a filin Wembley, lokacin da ya karbi kwallo daga wajen dan wasan da ya shigo sauyi Adam Lallana.

An zabi Raheem Sterling, dan kwallon da yafi fice a wasan, kafin kocin ya bayyana 'yan kwallon da zai zaba zuwa gasar cin kofin duniya a Brazil.

Hodgson ya ce "ina farincikin yadda 'yan wasan su ke nuna kwazonsu, da kishirwar neman shiga tawagar 'yan kwallon da za su buga mana a gasar kofin duniya."