Ina cikin tsaka mai wuya - Magarth

Felix Magarth Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Kocin ya ce yana cikin tsaka mai wuya amma zai yi iya kokarinsa

Kocin Fulham Felix Magarth, ya ce ceto kulob din kada ya fita daga gasar Premier bana, shi ne aikin horas wa mafi kalu bale da da ya fuskanta, amma ya bugi kirji cewa kungiyar za ta ci gaba da zama a gasar Premier.

Kungiyar tana matsayi na karshe a kasan tebur da maki 21, sauran wasanni goma a kammala gasar bana, kuma za ta ziyarci Cardiff ranar Asabar wacce take da tazarar maki guda tsakaninsu.

Magarth, wanda ya lashe kofunan Bundesliga na Jamus har sau uku ya ce "aiki ne mai wuya saboda mu ne a kasan Teburi kuma wasannin sun zo karshe.

Kocin shi ne dan Jamus na farko da yake horas wa a Premier, bayan da ya maye gurbin Rene Meulensteen ranar 14 ga watan Fabrairu, wanda ya jagoranci kulob din a wasanni 17.