Coleman ya yaba da wasan Bale

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin ya yi murna da yake horas da Bale a tawagar Wales

Kocin tawagar Wales Chris Coleman, ya yi barkwancin cewa kadan ya rage ya nemi sa hannun Gareth Bale, saboda yadda ya nuna kwazo a taka ledar da suka doke Iceland da ci 3-1.

Bale, ne ya baiwa James Collins da Sam Vokes kwallaye da suka zura a raga, sannan ya zura kwallo ta uku a raga.

Dan wasan Real Madrid, mai shekaru 24, shi ne dan kwallon da ya yi fice a wasan sada zumuncin da suka buga a filin Cardiff.

Coleman ya ce "dan wasa ne mai ban sha'awa -- nayi murna da yadda yake karfafawa 'yan kwallo gwiwa."