Zan so na dade da Ingila — Hodgson

Roy Hodson
Image caption Kocin na fatan tsawaita kwantiraginsa da tawagar Ingila

Kocin tawagar Ingila, Roy Hodgson, na fatan tsawaita aikinsa na horar da Ingila har karshen yarjejeniyar da suka kulla wadda zata kare a 2016 -- ko da Ingila ba ta taka rawa a kofin duniya ba.

Mai shekaru 66, ya rattaba hannu a kan kwantiragi na shekaru hudu da hukumar kwallon Ingila a Mayun 2012, ya kuma ce zai so ya tsawaita horar da tawagar bayan kofin zakarun Turai a shekarar 2016.

Hodgson ya ce "Zan yi aiki tukuru na cika yarjejeniyar da muka kulla, fatana FA ma ta cika alkawarin da ta dauka."

Kocin ya lashe wasanni 14 daga cikin wasanni 25 da ya jagoranci tawagar ta Ingila ta buga.

Ingila na rukuni mai tsauri a gasar cin kofin duniya, inda za ta fara karawa da Italiya ranar 14 ga Yuni, sai kuma Uruaguay ranar 19 ga Yuni da kuma wasan karshe na rukunin da Costa Rica ranar 24 ga Yuni.

Babu kasar da ta doke Ingila a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, ta samu tikiti bayan da ta jagoranci rukunin da ta taka.

Hodgson ya ce ba shi da masaniya a kan ko zai ci gaba da aikinsa bayan gasar cin kofin duniya.