FA: Hull ta doke Sunderland 3-0

hull vs sunderland
Image caption Karon farko da Hull ta kai wannan matsayi tun shekarar 1930

Kungiyar kwallon kafa ta Hull City ta samu kaiwa wasan daf da na karshe a kofin FA, bayan da ta doke Sunderland da ci 3-0 ranar Lahadi.

Curtis Davies ne ya fara zura kwallo da ka daga dukan kwana, sannan tsohon dan kwallon Sunderland David Meyler ya kara kwallo ta biyu da ya karba a kafar Lee Cattermole, ya arce har raga.

Dan wasan Sunderland Lee Cattermole ne ya sake yin kure, lokacin da ya maida kwallo gida nan take Matty Fryatt ya zari kwallon ya kuma buga daga yadi na 12 ta shiga raga.

Tun farko Sone Aluko ya barar da fenariti kafin a tafi hutun rabin lokaci, kafin daga baya kungiyar ta saka kaimin da ya kaita wasan daf dana karshe da za ta kara da Shieffield United a Wembley.

Wannan shi ne karon farko da Hull ta kai wasan daf da karshe a kofin FA tun shekarar 1930.