"Man City ce za ta iya lashe Premier"

Jose Morinho
Image caption Mourinho ya ce rikwon kwarya Chelsea ta ke yi a Teburin Premier

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce kofin Premier na Manchester City ne, da har yanzu su ke rikon kwaryar teburi, duk da doke Tottenham 4-0 da suka yi ranar Asabar.

Chelsea tana matsayi na daya ta bai wa City tazarar maki tara, sai dai City tana da kwantan wasanni guda uku.

Mourinho ya ce "Zai fi dacewa a ce mu ne a matsayin City, da zarar sun lashe kwantan wasansu kofin bana ya zama nasu."

Sauran wasanni tara a kammala gasar bana, Chelsea ta bai wa Liverpool da Arsenal tazarar maki bakwai duk da suna da kwantan wasa guda daya.